Gwaje-gwajen shirye-shiryen mu

Masu sauraro, muna matuqar farin cikin kasancewar ku tare da mu a wannar tasha ta Muallim Rediyo, mai nufin ilimatar da mai sauraro akan abubuwa na addinin musulunci.

A halin yanzu muna gwaje-gwaje na kayan aikin mu da kuma kokarin tattaro muku shirye shirye masu amfani, ni shadan tarwa da ilimantarwa.

Zaku iya aiko mana sako ta hanyar whatsapp kai tsaye in an latsa logo din whatsapp a shafukan mu na internet. Domin jin ra’ayin ku da kuma shawara da baiyana nau’in shirye shiryen da kuke bukatar ji da kuma lokutan da kuke bukatar son jin shirye shiryen.

Muna kara godiyar kasancewar ku tare da mu. Muna sauraron shawarwarin ku da sakonnin ku.

Bissalam,

Mu’allim

Lale Marhaban – Barka da zuwa Al-Muallim Radio

Assalamu Alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu, barka da zuwa wannan shafi na Al-Mu’allim Radio.

al-Mu’allim Radio, rediyo ne da aka samar da shi domin yin hobbasa wajen kawo ilimi ga masu sauraro, ta hanyar kawo KaratunTafsiri, Karatun Hadisai, Muhawara, Muqala, Qasida da sauran makamantan su.

Wannan rediyo za’a same ta hanyar internet a shafin mu www.muallimradio.ml ko a app din Tunein da makamantansu.

× How can I help you?